DA DUMI-DUMI: Pantami Yayi Watsi da Dokar Gidajen Abuja, Ya Kawo Babban Janareta na Miliyoyin Nairori


Mazauna wani katafaren yanki da ke Unguwar Jaji-Kado a Abuja sun yi Allah-wadai da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dakta Isa Ali Pantami kan karya dokar unguwar kan amfani da janareta.

Pantami ya dauki babban janareta zuwa sabon gidansa na miliyoyin naira a yankin.
 
Sun ce duk da bayyana wa Pantami cewa amfani da janareta ya saba wa ka’idar gidan, ya kawo daya da rana domin ya nuna musu ya fi karfin doka.

A halin da ake ciki, Minista Pantami na cigba da shan suka daga 'yan Nijeriya, tare da fatan a tsige shi saboda rashin katabus da tsinana abun arziki.

Post a Comment

Previous Post Next Post